1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin shugaban ƙasar Nijar kan harin da aka kai Agadez

May 25, 2013

Shugaban ƙasar Nijar ya ce harin da aka kai Agadez bai baiwa hukumomin ƙasar mamaki ba, sai dai daga yanzu za su zage dantse wajen tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin 'yan ƙasa

https://p.dw.com/p/18dz1
epa02847783 President Mahamadou Issoufou of Niger during a meeting with US President Barack Obama and fellow African leaders from Niger, Benin, and Guinea, in the Cabinet Room of the White House, in Washington DC, USA, 29 July 2011. EPA/MARTIN H. SIMON / POOL +++(c) dpa - Bildfunk+++
Mahamadou IssoufouHoto: picture alliance/dpa

A karon farko tun bayan hare-haren da wasu ƙungiyoyin masu tsananin kishin addinin Islama su ka kai a garuruwan Agadez da Arlit, da ke a yankin arewacin ƙasar Nijar, shugaban ƙasar Alhaji Mahamadu Isufu ya yi magana, inda ya nuna takaicinsa da afkuwar lamarin wanda ya ce bai ba su mamaki ba amma kuma za su ci gaba da yakar kungiyoyin 'yan ta'adar.

Shugaban ƙasar ta Nijar ya kuma jinjinawa sojojin ƙasar dangane da abun da ya kira jarumtakar da su ke ci gaba da nunawa wajen gudanar da ayyukan tsaron 'yan Nijar da dukiyoyinsu.

Shugaban ƙasa Alhaji Mahamadu Yusufu ya yi wannan bayani ne a gaban manema labarai, jim kadan bayan ganawarsa da babban darektan kamfanin AREVA Luc Oursel wanda ya kai wata ziyara ƙasar domin ganewa idanunsa irin ɓarnar da harin da aka kaiwa cibiyarsu na haƙan ma'adinin Uranium ya yi, da ma kuma tattaunawa da shugaban ƙasar a kan sabbin matakan tsaron da ya kamata su dauka

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba'
Edita: Umaru Aliyu