1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Tawagar AU game da zaɓen Yuganda

February 22, 2011

Tawagar AU a zaɓen Yuganda ta ce ƙasar bata gudanar da sahihin zaɓe ba

https://p.dw.com/p/10Lsw
Shugaba Yoweri Museveni na YugandaHoto: DW/Schlindwein

Tawagar ƙungiyar Tarayyar Ƙasashen Afirka ta AU wadda ta sa ido a kan yadda aka gudanar da alamurar zaɓe a Uganda, ta ce an samu kura kurai da dama, a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a makon da ya gabata, a yayin da 'yan takara biyu suke neman a ƙaddamar da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati, irin wanda ke afkuwa a ƙasashen Larabawa.

Shugaba Yoweri Museveni wanda ke jan ragamar mulkin Uganda na tsawon shekaru 25 yanzu, ya lashe zaɓen ne da kashi 68 cikin ɗari na yawan ƙuri'un da aka kaɗa, a yayin da babban abokin hammayar na sa, Kizza Besigye ya sami kashi 26.

Shugaban tawagar, Gitobu Imanyara ya bayyana cewa mutane da yawa da suka cancanci yin zaɓe basu sami daman kaɗa ƙuri'ar su ba, saboda rashin kyakyawan tsari a wuraren jefa ƙuri'un.

Tuni dai ɓangaren Museveni suka ƙaryata zargin cewa an sami kurakurai a zaɓen, ko da yake abokan hammayar Musevenin sun yi barazanar ƙaddamar da zanga-zangar nuna adawa da gwamnati, amma Museveni ya yi barazanar ɗaure duk wanda ya tayar da wani tashin hankali a kurkuku.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar