1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin 'yan Najeriya kan tattaunawar Buhari da Trump

February 14, 2017

Bayan tattaunawa tsakanin Shugaban Amirka Donald Trump da Shugaba Muhammadu Buhari, akwai sabon fata tsakanin 'yan kasar da gwamnati bisa dangantakar mai tasirin gaske.

https://p.dw.com/p/2XXEA
Nigeria Muhammadu Buhari Präsident Rede vor der UN Vollversammlung
Hoto: Getty Images/AFP/M. Ngan

Babu dai zato ba kuma tsammani Shugaba Donald Trump ya yanke shawarar ganawa da wasu a cikin shugabannin nahiyar Africa a karon farko tun bayan hawansa mulki a tsakiyar watan Janairun da ya gabata. Abun kuma da ya  haifar da sabon fata kama daga mahukuntan Najeriya ya zuwa yan kasar da a baya ke kallon mulkin na Trump din mai hadarin gaske ga makomar rayuwar al'uma.

Ganawar da ta mayar da hankali ga muhimman batutuwan ta'addanci da batu na tattalin arziki dai, daga dukkan alamu ta kwantar da hankula cikin tarrayar Najeriyar da a baya ke tunanin ta zo karshen bayan kare wa'adin mulkin tsohon shugaban kasar amirka Barrack Obama.

Tattaunawa mai tasiri ga yaki da tarzoma

Tuni ma fadar gwamnatin Najeriyar ta kira tattaunawar a matsayin mai tasiri da kuma ta kwantar da fargaba. Kamar yadda malam Garba Shehu da ke zaman kakaki na gwamnatin ta Abuja ya nunar.

USA Donald Trump und Michael Flynn in Palm Beach
Hoto: Reuters/C. Barria

Sai dai in har ana shirin dorawa a cikin danyen ganyen dai, amincewar Amurkan na cinikin makamai ga tarrayar Najeriyar dake fatan kare yakin Boko Haram cikin sauri ya kara karfin gwiwa dama kawar da tunanin mummunar manufa a bangaren Shugaba Trump din ga kasashe irin su Najeriyar a fadar Dr. Kole Shettima da ke zaman shugaban cibiyar demokuradiyya da ci gaba dake Abuja.

In har ana shirin hange na wuta a masaka, dai har  ya zuwa yanzu kuma a fadar Ambassada muhhamad kawu ibrahim dake zaman wani tsohon jamií na jakadanci, sabon shugaban na Amurka na zaman mazarin da gabansa ke da wuyar ganewa, abun kuma da yasa da sauran tafiya kafin iya kaiwa ga kwantar da hankali da mulkin nasa.