Masar da Qatar za su jagoranci sulhun tsagaita wuta a Gaza
February 7, 2024A Alhamis din nan ce Masar da Qatar za su jagoranci fara wata sabuwar tattaunawar tsagaita wutar rikicin Gaza a birnin Alkahira, tare da musayar fursunoni, kamar yadda wani jami'in gwamnatin Masar din ya sanar wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Karin bayani:Gaza: Kokarin tsagaita wuta mai dogon zango
Haka zalika wani jami'in kungiyar Hamas ya tabbatar wa AFP amincewarsu da yarjejeniyar tsagaita wutar, tare da musayar fursunoni. Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce rikicin na watanni 4 ya yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa 28,000.
Karin bayani:Majalisar Dinkin Duniya ta ce yunwa na kisa a Gaza
Yanzu haka dai sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken na ziyararsa karo na biyar a yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan barkewar yakin, a kokarin ganin an kawo karshensa.