1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Anyi Allah wadai da yan tawayen Houthi

Zulaiha Abubakar
June 16, 2019

Gwamnatin Masar ta yi Allah wadai da harin da 'yan tawayen Houthi suka kai wa filayen jirgin saman Kasar Saudiya da ke biranen Abha da Jizan.

https://p.dw.com/p/3KXmi
Griechenland Ägyptischer Präsident Al-Sisi
Hoto: Reuters/Y. Kourtoglou

Dama dai tuni 'yan tawayen suka sanar da alhakin kai harin da nufin daukar fansa ko da yake Saudiya ta tabbatar da harbo wani jirgi maras matuki mallakar 'yan tawayen na Houthi, Kasar ta Masar dai guda ce cikin kasashen da ke goyon bayan gamayyar sojojin kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiya wadanda kuma ke yaki da 'yan tawayen a kasar Yemen tun a shekata ta 2015.