1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Ana lullube makamai cikin abinci zuwa Gaza

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Abdul-raheem Hassan
January 16, 2024

Hukumomin tsaro a kan iyakar Masar da Gaza sun tabbatar da mutuwar mutum daya, yayin dakile masu yunkurin fasakwaurin kwayoyi da makamai a nisan kilomita 40 da mashigin Rafah.

https://p.dw.com/p/4bI0J
Hoto: Mohammed Talatene/dpa/picture alliance

Rundunar sojin Masar ta dakile wani yunkurin fasakwaurin makamai da muggan kwayoyi a kan iyakarta da kasar Isra'ila, lokacin binciken kayan agajin da ake kai wa Zirin Gaza.

Karin bayani:Mutane fiye da 24,000 suka rasu a yakin Gaza

Hukumomin sun  tabbatar da mutuwar mutum daya, yayin da aka kama masu yunkurin fasakwaurin su 6, a kan iyakar ta Al-Awja, kilomita 40 da mashigin Rafah, da Isra'ilawa ke kira da Nitzana.

Karin bayani:WHO na son ba ta hanyar iya kai agaji a Zirin Gaza

A ranar 7 ga watan Okotoban shekarar 2023 ne dai kungiyar Hamas ta kai hari kan Isra'ila, lamarin da ya janyo mutuwar mutane 1,400, mafarin sabon rikicin kenan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa sama da dubu 24,000.