1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta yanke dangantaka da Siriya

June 16, 2013

Shugaban Masar Mohamed Mursi ya sanar da hakan, tare da nuna goyon bayansa ga shirin Amirka na sanya takunmin zirga-zirgar jiragen sama a wasu sasssan kasar.

https://p.dw.com/p/18qoh
Egypt's President Mohamed Mursi delivers a speech at a Syria solidarity conference organised by the Muslim Brotherhood, in Cairo, in this handout picture taken June 15, 2013, and provided by the Egyptian Presidency. Mursi said he had cut all diplomatic ties with Damascus on Saturday and demanded Hezbollah leave Syria, pitching the most populous Arab state more firmly against Syrian President Bashar al-Assad. REUTERS/Egyptian Presidency/Handout (EGYPT - Tags: POLITICS TPX IMAGES OF THE DAY) ATTENTION EDITORS – THIS IMAGE WAS PROVIDED BY A THIRD PARTY. NO SALES. NO ARCHIVES. FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS PICTURE IS DISTRIBUTED EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Hoto: Reuters

Da ya ke jawabi ga wani taron muzahara da malaman Sunna su ka kirawo a kasar, Mursi ya kuma bukaci kungiyar Hezbollah ta Labanon ta daina sanya baki cikin yakin na Siriya.

A nata bangaren Rasha da ke zaman babbar kawa ga gwamnatin Siriya, cewa ta yi duk wani yunkuri na sanya takunkumin hana zirga-zirgar jiragen sama a Siriya ya saba wa doka.

Da ta ke maida martani kan jawabin na Mursi gwamnatin Siriya, ta yi tir da matakin da ya dauka na yanke hulda da Damaskus din, da kuma nuna goyon bayansa ga shirin kakaba mata takunkumin hana zirga-zirgar jiragen sama da baiwa 'yan tawayen da ke yakar gwamnatin Bashar al-Assad kananan makamai, suna mai cewa hakan wani mataki ne da bai da ce ba.

Mawallafiya : Lateefa Jaafar Mustapha
Edita            : Zainab Mohammed Abubakar