Masoud Pezeshkian ya lashe zaben Iran
July 6, 2024Talla
Masoud Pezeshkian ya samu nasarar lashe zaben kasar Iran da kuru'u miliyan 16, inda abokin karawarsa Saeed Jalili ya samu kuru'u miliyan 13 a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Juma'a.
Karin bayani: Ana gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Iran
Shugaban mai shekaru 69 da haihuwa da ke zama tsohon ministan kiwon lafiya ya yi alkawarin kawo gagarumin sauyi ga kasar a idon duniya. Sai dai duk wani buri da ake tsamannin ya zai kawo a siyasar cikin gida da ta kasashen waje, cikakken iko na zartar da komai na hannun jagoran juyin juya halin kasar Ayatullah Ali Khamenei.