110912 NSU Untersuchungsausschuss MAD
September 12, 2012Komitin bincike da Majalisar Dokokin Jamus ta kafa game da baddaƙalar leƙen asiri akan 'yan Nazi ya gano cewar hukumomin leƙen asirin ƙasar sun ɓoye bayanai kan masu wariya da suka yi kashe kashe a shekarun baya. Wani tsohon jami'in leƙen asiri mai suna Uwe Mundlos ne ya fasa ƙwai lokacin da ya ke bayar da bahasi gaban wannan komiti.
Shi dai Uwe Mundlos ya shafe watannin da dama ya na kula da al'amuran da suka shafi 'yan nazi a shekarun 1990. Sai dai kuma hukumar leƙen asiri da ya ke wa aiki ta taɓa tambayarsa ko daidai da rana ɗaya zai taɓa tona asirin masu ƙyamar baƙi da ke kashe-kashen ba gayra? Amsar da ya bayar dai itace a'a. Ko da a lokacin da ya bayar da bahasi gaban shugaban kwamitin bincike da majalisa ta kafa Sebastien Edathy, sai da ya sake nanata wannan matsayi na sa. Lamarin da ya sa 'yan majalisan ke ganin cewar hukumomin leken asirin Jamus su yi rufa rufa game da kashe kashen da 'yan nazi suka aikata a baya. Amma kuma shugaban hukumar asiri da ke karkashin majalisar sojoji ta Bundeswehr wato Ulrich Birkenheier ya ce babu kamshin gaskiya a cikin wannan furuci.
"Hukumar leƙen asiri ta MAD ba ta taba sanya Mundlos a sahun waɗanda suke da masaniya game da wannan batu ba."
Sai dai kuma daga watan Afirilun 1994 zuwa Maris na 1995 Mundlos ya yi bautar ƙasarsa a wani barikin sojiji na birnin Thüringen, inda ya yi ma'amala da kiɗe-kiɗen 'yan nazi. Bayannan da wannan sojan ya yi sun bai wa shugaban kwamitin bincike samun masaniya game da ɗaurin gindi da 'Yan Nazi suka samu daga hukumomin leƙen asirin Jamus ciki kuwa har da wadda ke ƙarƙashin sojoji. Da ma dai kwamitin ya samu bayanai game da takardun shaida da hukumar ta MAD ta kona waɗanda ke nunawa ƙarara cewar suna ɗasawa da 'yan Nazi
Sai dai kuma tun a watan Maris na wannan shekarar, hukumar da ke kare tsarin mulki ta sami shaidar da ke nuna alakar da ke tsakanin masu kyamar bakin na Jamus da kuma abokan burminsu na hukumomin leƙen asiri. Bayanan da wakiliyar jami'yar Linke a kwamitin ta ce ba ta san da su ba a baya.
"A fili ya ke cewar MAD da sauran hukumomin leken asiri sun sharamin karya game da wannan batu."
Dan majalisa Christian Ströbele da aka zaba karkashin inuwar jam'iyar The Greens ne ya bukaci a zurfafa wannan bincike game da zargin rufa ruda da ake yi ma hukumomin leken asiri na Jamus. Tuni dai shugaban babbar hukumar leken asiri ya yi murabus bayan da aka gano cewar jami'ansa sun rafa ma wasu 'yan nazi biyu da suka kashe kashen ba gaira asiri iya tsawon rayuawansu.
Su dai 'yan majalisan na jamus suna neman sanin waɗanda suka ƙona bayanai game da wasu 'yan nazi da suka kashe turkawa da dama a shekarun 1990. Sannan kuma daga bisani su yi tankaɗe da rairaya tare da yi ma hukumomin leƙen asirin na ƙasar Jamus gyran fiska.
Mawallafi: Mouhamdou Awal Balarabe
Edita:Yahouza Sadissou Madobi