Masu bukata ta musamman na son kulawa
May 6, 2020Talla
Babban sakataren ya baiyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya nuna goyon baya ga wani nazari da Majalisar Dinkin Duniyar ta gudanar kan mutane masu bukata ta musamman.
Mr Guterres ya ce annobar corona ta kara samar da wagegen gibi na rashin daidaito da haifar da sabbin barazana.
Ya kara da cewa ko a lokacin da hankalin duniya ke kwance ire-iren wadannan mutane masu bukata ta musamman akan manta da su, wanda hakan ke tauye musu hakkin samun ilimi da ingatancen tsarin lafiya da ma damar bada tasu gudumawa a yankunansu.