Helena Marschall da Jacob Basel 'yan fafutikar kare muhalli da ake kira "Fridays for Future" ne, sun halarci zanga-zangar da ta fito da sunan fafutikar kare muhallin da ake shirya wa kowace Juma'a. Annobar Coronavirus ta sa an dakatar da tarukan, a yanzu masu fafutikar na nazarin sabbin hanyoyin fadakarwa.