Masu rikici da juna a Sudan na tattauna batun tsagaita wuta
July 12, 2024Bangarorin da ke rikici da juna a Sudan sun gudanar da tattaunawa a birnin Geneva kan batun kare fararen hula da tabbatar da isar da kayan agaji a kasar. Majalisar Dinkin Duniya wacce ke shiga tsakanin sojojinSudan da dakarun sa kai na RSF ta ce abokan gaban na fatan ganin an tsagaita bude wuta. Sai dai Majalisar ta Dinkin Duniya ta jaddada cewar tattaunawar ba ta kai tsaye ba ce.
Karin bayaniFatan tattaunawa don kawo karshen rikicin Sudan:
An dai kwashe sama da shekara guda ana gwabza fada a Sudan tsakanin sojoji da dakarun sa-kai, kuma rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 14,000 yayin da mutane 33,000 suka ji raunuka a cewar alkalumman Majalisar Dinkin Duniya. Kazalika kusan mutane miliyan 25 wato fiye da rabin al'ummar Sudan na bukatar taimako yayin da kusan mutane miliyan 18 na fuskantar matsalar karancin abinci.