Mata mafi kwarewa a kwallon kafar duniya
Za a karrama gwarzuwar wasan kwallon kafa ta duniya da kyautar Ballon d’Or a tsakiyar watan Oktoba. Tare da Alexandra Popp da Lena Oberdorf, 'yan wasan Jamus biyu su ma suna cikin zaratan 'yan takara a gasar.
Alexandra Popp
'Yar wasan ta dauki lokaci mai tsawo tana murmurewa daga raunin da ta ji a kakar wasan da ta wuce, amma a gasar cin kofin Turai a Ingila ta nuna bajinta a tawagar kasar Jamus: "Poppi" tana zura kwallaye a kalla a ko wane wasa, amma gabanin kammala gasar ta samu rauni. Sau biyu Popp tana lashe gasar tare da VfL Wolfsburg.
Lena Oberdorf
'Yar wasan baya ta zo ta biyu a bangaren Popp kuma an san ta a matsayin mafi bajintar matashiya 'yar wasa a gasar. Ta lashe gasar Jamus tare da VfL Wolfsburg kuma tana murnar nasara a gasar cin kofin kwallon kafa. A gasar zakarun Turai, a gefe guda, Oberdorf da "wolf" sun kara a wasan kusa da na karshe da FC Barcelona.
Lucy Bronze
A kakar wasa ta 2021/22, mai tsaron bayan Manchester City ta dade tana fama da rauni. Kulob din ya kare a matsayi na uku a gasar Super League ta kasar Ingila. Kambun kakar wasa shi ne nasara a gasar cin kofin Turai a cikin gida. Ana saka Bronze cikin filin wasa a duk wasanni, inda take zura kwallo daya kuma tana ba da taimako. Bayan gasar cin kofin Turai ta koma Barcelona.
Alex Morgan
A gasar Olympics da aka yi a Tokyo a bara, Alex Morgan ta so ta lashe gasar Olympics tare da tawagar Amirka, amma ta kasa a wasan kusa da na karshe da Kanada kuma a karshe ta koma gida da tagulla. A gasar kwallon kafa ta mata ta Amirka, zakaran duniya sau biyu tana taka leda a San Diego Wave FC tun farkon wannan shekara kuma tana yawan zura kwallo a raga.
Christiane Endler
Ita ce 'yar kasar Chile mai tsaron gida daya tilo a cikin jerin sunaye 20 da aka tantance na ‘yan takarar Ballon d’Or. Bayan zama a Chelsea, Valencia da Paris St. Germain, ta kasance tana taka leda a Olympique Lyonais tun bazarar 2021. Tare da OL a cikin 2022, ta zama zakarar Faransa kuma ta lashe gasar zakarun Turai. A shekarar 2021 ta zama Gwarzuwar gola a duniya na FIFA.
Alexia Putellas
Ta samu nasara a wasanni 30, inda ta ci kwallaye barkatai- kyaftin Alexia Putellas ta jagoranci FC Barcelona zuwa gasar. A gasar cin kofin zakarun Turai, duk da haka, an sha kashi a hannun Lyon. Jim kadan kafin gasar cin kofin nahiyar Turai, Putellas ta sake samun koma-baya: raunin da ya faru kwanaki uku kafin a fara gasar.
Aitana Bonmati
Aitana Bonmati abokiyar tarayya ce ga Putellas a tsakiya da kuma mai kai hari a tsakiya - duk a FC Barcelona da kuma cikin tawagar kasar Spain. Tun tana da shekaru 13 ta shiga karamin sashin Barcelona. Tana da shekaru 17 ta fara fitowa a cikin tawagar farko. Idan ba tare da Putellas ba, ba za ta iya hana cin nasara a wasan daf da na kusa da na karshe da Ingila a gasar Euro ba.
Asisat Oshoala
Da kwallaye 20 a kakar wasa ta bana, Asisat Oshoala ta fi Putellas nasara. 'Yar Najeriya ta raba kambun wanda ya fi zura kwallaye tare da dan kasar Brazil Geyse Ferreira na Real Madrid a kakar wasan bara a gasar La Liga. An zabi Oshoala a matsayin gwarzuwar 'yar kwallon Afrika a karo na biyar a wannan shekara.
Fridolina Rolfö
Tsohuwar 'yar wasan FC Bayern da VfL Wolfsburg ta zama jigo a harin Barça Femeni. Ba kamar a Bundesliga ba, 'yar kasar Sweden ta fi fice a Spain a matsayin wacce ta shirya. A gasar Euro ta kai wasan kusa da na karshe tare da 'yan kasar Sweden, amma ta samu nasarar cin kwallo daya kacal da kanta.
Millie Bright
Mai basirar tsare gida ko yaushe tana zuwa inda ya yi zafi. Tare da Chelsea a 2022 ta lashe gasar zakarun Turai sau biyu da kuma gasar cin kofin FA a Ingila. Amma wannan abin takaici ya wuce yadda Bright ta lashe gasar Euro da Ingila.
Beth Mead
Yayin da Bright ke share kwallayen da ke bayan gasar cin kofin Turai, Beth Mead ta jefa kwallo ta gaba. 'Yar wasan ta Arsenal ta zura kwallaye shida a gasar ta "Lionesses". An zabe ta a matsayin wadda ta fi zura kwallaye kuma ’yar wasa a gasar. Tare da kulob dinta, Mead ta yi rashin nasara a gasar zakarun da maki daya a bayan Chelsea.
Vivianne Miedema
'Yar Holland din ta kasance abokiyar wasan Mead a Arsenal FC. Ta ci kwallo 14 a kakar wasan da ta wuce a gasar cin kofin mata. Gasar Euro ta Ingila ba ta tafi kamar yadda aka tsara na tsohuwar yar wasan Bayer ba. A wasan farko,taa samu rauni. Ba za ta iya sake buga wasan daf da na kusa da na karshe da Faransa ba, amma ta ci gaba da zama ba tare da cin kwallo a gasar cin kofin Turai ba.
Sam Kerr
Sam Kerr ne kawai ta fi Miedema nasara a cikin jerin masu zura kwallaye na Super League. 'yar wasan 'yar kasar Ostareliya ta ci wa Chelsea kwallaye 20 a wasanni 22 da ta yi kuma ta taka rawar gani wajen lashe gasar. A wasan karshe na cin kofin FA da Manchester City, Kerr ta yi 1-0 sannan kuma abu mai muhimmanci ta ci 3-2 a cikin karin lokaci. An zabe ta a matsayin gwarzuwar ‘yar wasan Ingila.
Ada Hegerberg
'Yar kasar Norway ta kasance mace ta farko da aka ba kyautar Ballon d'Or a shekarar 2018. A cikin 2022 ta lashe gasar Faransa ta bakwai da kuma ta shida a gasar zakarun Turai tare da Olympique Lyonais. Gasar Euro kawai ta zama mai sauki ga Hegerberg da kungiyar ta Norway. Daga cikin wasu abubuwa, bayan 0:8 da Ingila ta yi, ya zama kammala wasan share fage.
Wendie Renard
Al'amura suna tafiya ga abokiyar wasan Hegerberg Wendie Renard da ta dade a gasar cin kofin Turai. 'Yar wasan baya mai tsayin mita 1.87, wanda ko da yaushe ta yi kama da mai yin wasan gaske, ta gaza tare da Faransa a wasan kusa da na karshe da ta fuskanci tawagar Jamus. Renard ta zama zakaran Faransa sau 15 kuma ta lashe gasar zakarun Turai sau takwas.
Marie-Antoinette Katoto
A wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai da Jamus, ba ta nan. 'Yar wasan da ta fi zura kwallaye a ragar Faransa a watannin baya ta samu rauni a gwiwarta a wasan rukuni na biyu na gasar cin kofin nahiyar Turai. A baya can, Katoto ta gamsu tare da kima mai ban sha'awa. Ta lashe kofin ne tare da kungiyarta ta PSG, kuma ita ce ta fi zura kwallaye a gasar Faransa.
Kadidiatou Diani
Kadidiatou Diani abokiyar wasan Katoto ce a PSG da kuma tawagar kasar Faransa. Gwarzuwar 'yar wasan Faransa na shekarar 2021 na daukar matakinta na farko cikin kwarewa tun tana karama. Tana da shekaru 15 ta fara fitowa a rukunin farko. Amma Diani tana kula da wasanninta a waje: tana cikin kwamitin zartarwa na kungiyar kwararrun 'yan kwallon Faransa UNFP tun Nuwamba 2020.
Selma Bacha
Selma Bacha ta kasance tana taka leda a Olympique Lyonais tun tana da shekaru takwas. Yanzu tana da shekaru 21 kuma ta riga ta lashe gasar Faransa sau hudu tare da OL, da kuma kofuna hudu a gasar zakarun Turai. A gasar Euro 2022, Bacha, wanda ke aiki a bangaren hagu a cikin kungiyar Faransa, ta tike a wasan kusa da na karshe.
Catarina Macario
Catarina Cantanhede Melonio Macario, kamar yadda ake kiran ta 'yar Brazil da cikakken sunanta, tana wasa tare da Bacha a tsakiyar fili a Olympique Lyonais tun daga Janairun 2021. Tun tana karama ta yi hijira zuwa Amirka tare da danginta, inda ta samu kwarewar wasan kwallon kafa a makarantar sakandare da kwaleji. Macario yanzu Ba- Amirkiya ce kuma 'yar wasan kungiyar kasa.
Trinity Rodman
Trinity Rodman, wanda mahaifinta Dennis ya shahara a fagen kwallon kwando, ita ma tana buga wa tawagar Amirka wasa. Yayin da zakaran NBA ya kasance daya daga cikin mafi kyawun masu tsaron gida, 'yarsa tana wasa a kai hari. A 2021 ta fara buga wasan kwallon kafa na kwararru. A matsayinta na 'yar wasa mafi girma da ake biyan kudi a cikin kungiyar kwallon kafa ta Mata ta Amirka NWSL.