Mata sun samu izinin tukin mota a Saudiyya
September 27, 2017Rahotanni daga Saudiyya na cewa mahukuntan kasar sun sanar da shirin bai wa mata izinin tukin mota a kasar wacce ke zama daya-dayar kasa a duniya da mata ba su da wannan hurumin tukin mota a cikinta.
Kamfanin dillancin labaran Saudiyya na SPA ya ce mahukuntan Saudiyyar sun bayyana wannan aniya tasu ce a cikin wani kudurin doka da Sarki Salman ya dauka, inda ya ba da umurnin ba da lasin tukin mota ga mata da maza ba tare da bambanci ba. Dokar bai wa matan izinin tukin motar za ta soma aiki daga watan Yunin shekara ta 2018.
Tuni dai wannan mataki ya soma samun goyon baya a ciki da ma wajen kasar ta Saudiyya. Fadar White House a Amirka ta bakin kakakinta Nauert Holding ta yaba wa mahukuntan Saudiyyar da daukar wannan mataki tana mai cewa:
"Muna farin ciki da jin wannan labari wanda ya zo mana yanzu-yanzun nan, kuma lalle muna ganin wannan mataki da suka dauka ci gaba ne kuma babban alheri ne"
Mahukuntan Saudiyyar na tsare da wasu mata 'yan fafutika da a baya suka yi yunkurin keta dokar da ta haramta mata tukin mota a kasar a baya.