John Mahama ya sake dawowa madafun ikon Ghana
December 8, 2024Mataimakin shugaban kasar Ghana kuma 'dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NPP Mahamudu Bawumia ya rungumi kaddara a zaben, har ya taya tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama murnar samun nasara ta wayar tarho.
Karin Bayani: An fara kirga kuri'un zaben shugaban kasa a Ghana
Mahamudu Bawumia ya ce duk da yake ba a sanar da sakamakon zaben a hukumance ba, to amma alkaluman da ya samu sun nuna cewa Mahama ne ya samu nasarar lashe zabe, a don haka jam'iyyar ta NPP za ta mutunta ra'ayin al'ummar Ghana da suka zabi canji.
Har yanzu ba a kai ga sanar da kammalallen sakamakon zaben shugaban kasar ba, amma jam'iyyar adawa ta NDC ta sanar da cewa 'dan takararta ne ke kan gaba da kaso 56 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da take da kujeru 185 na kujerun majalisar dokokin kasa, daga cikin 276 da ake da su baki-daya. Tabarbarewar tattalin arziki na daga cikin matsalolin da suka yi wa Ghana tarnaki, inda ta fada tarkon bashin asusun ba da lamuni na duniya IMF.