Kotu ta dauki mataki kan hana gurbata muhalli
May 26, 2021Wata kotu da ke birnin The Hague ta kasar Holland ce, ta yanke hukunci, inda ta umarci kamfanin man na Shell da ya mutunta ka'idojin da yarjejeniyar birnin Paris ta cimma a game da yawan iska mai dauke da sinadarin carbon da ya ke fitarwa. Kotun da ke kasar Netherland ta ce, dole Shell ta soma aiki da wannan umarnin, kafin nan da shekarar 2030, inda ake son iskar carbon da kamfanin zai fitar, kada ya fice kashi 45 cikin dari.
A dai shekarar 2018, wasu kungiyoyi na masu rajin kare muhalli da kungiyar kare hakkin dan adam da wasu 'yan kasar Netherlands sama da dubu daya da dari bakwai, suka shigar da karar kamfanin na Shell a gaban kotun, bisa zarginsa da kin mutunta yarjejeniyar, abin da suka ce ya taimaka, a karuwar matsalar gurbata muhalli a duniya. Wannan na daya daga cikin kararraki da masu rajin kare muhalli suka shigar a sassa daban daban, don ganin an rage iskan mai hadari da jama'a ke shakka,masana kimiyya dai sun ce dole iskar da ake fitarwa ta ragu sosai, domin a samu daidaito a yanayin muhalli.