1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNajeriya

Kano: Matakin hana yara bara

January 2, 2025

Jihar Kano ta fara tattara yara 'yan gararamba da nufin mayar da su ga iyayensu, domin su samubkyakkyawar tarbiyya da kuma rayuwa mai kyau a nan gaba.

https://p.dw.com/p/4olOS
Najeriya | Kano | Yara | Bara | Tsangaya
An dai jima ana son daukar matakin alkinta makarantun allo domin hana yara baraHoto: DW

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake tattara kan wadannan yara a mayar da su ga iyayensu ba, amma kuma hakan ba ya hana su dawowa ko kuma samun sababbin yara da ke bara a kan titunan jihar Kano ba. Shugaban Hukumar Hisbah ta jihar Kanon Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya nunar da cewa, sun dauki wannan mataki ne domin smarwa da yaran makoma mai kyau a nan gaba. Irin wadannan yara sama da 200 da suka kasance 'yan asalin jihar ta Kano da ma sauran jihohi har ma da na ketare hukumar ta tattara a masaukin alhazai na jihar, kafin ta kammala tsare-tsaren mayar da su ga iyayensu. Irin yadda wadannan yara ke gararamba a kan tituna da mafi yawa ba 'yan asalin jihar ba ne, ya jima yana ci wa al'umma tuwo a kwarya. Wannan ya sanya al'ummar na ganin ya kamata a dauki mataki na din-din-din, ba na je ka ka dawo ba da yaran ke zuwa suna dawowa.