Matakin Japan game da abinci mai guɓa
March 23, 2011Gwamnatin Japan ta haramta wa al'uma amfani da madara da kuma duk wani nau'in abinci da aka shuka a birnin Fukushima da kuma kewayensa. kana ta dakatar da jigilar kayan lambu da kuma abinci gwagwani da ake sarrafawa a birnin da cibiyar nukuliyarke kafe, zuwa wasu sassa na ƙasar da ma dai ƙetare. Wannan matakin ya biyo bayan nuna damuwa da hukumar makamashin nukiliya ta duniya ta yi, dangane da wani burbushin sanadari da ke fita daga tashar nukuliya ta Fukushima. Hukumomi ba su kai ga tantace guɓar da ke tashi daga sunduƙan da suka tarwatse tare da fitar da hayaki ba.
Hukumnomin na Japan sun bayyana cewar wata girgizar ƙasar ta sake afkuwa a kewayen Fukushima ba tare da haifar da salwantar rayuka ko kuma lalata kadarori ba. Sama da mutane 9300 ne girgizar ƙasa da kuma ambaliyar Tsunami ta ritsa da rayakunsu makwanni biyun da suka gabata. yayin da mutane kusan dubu 14 suka rasa matsugunansu a tagwayen bala'o'i daga indalalhi da Japan ta fiskanta.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar