Matan da aka sace a jihar Borno sun zarta 100, in ji hukuma
March 7, 2024Jami'in yada labarai na karamar hukumar Ngala Ali Bukar ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa mazauna kauyen sun tabbatar da bacewar mutane 113 a halin yanzu. Dama ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya ce an yi garkuwa da mata sama da 200 da ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira a lokacin da suka je neman itace.
Karin bayani: Kokarin magance tsaro a arewacin Najeriya
Satar mutane don neman kudin fansa na ci gaba da zama babbar matsala a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso gabashin Najeriya. Shugabannin mayakan sa-kai na zargin kungiyar ISWAP da marar hannu a satar mutane. Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya hau karagar mulki ne a 2023 ya yi alkawarin magance tabarbarewar tsaro da kuma barkewar rikicin kabilanci a jihohin tsakiyar kasar.
Karin bayani: Najeriya: Ina kudaden fansa suke shiga?
A Jihar Borno dai, ayyukan ta'addanci sun yi sanadin mutuwar mutane sama da 40,000 tare da raba miliyan biyu da muhallansu a cikin shekaru 15 da suka gabata.