Matan da ke jagorantar yaki da coronavirus
Daga jajirtaccen shugabanci zuwa binciken magunguna da ba shi da iyaka, wadannan mata na jagorantar fafutukar dakile annobar COVID-19.
Ba sani ba sabo- Angela Merkel
Jamus ta yi fice a kanun labaran duniya, dangane da yadda ta dauki matakan yaki da coronavirus, musamman karancin wadanda ke mutuwa. An yabawa shugabar gwamnati, dangane da yin gargadin cewa kaso 60 cikin 100 na al'ummar kasar ka iya kamuwa, ba tare da boye-boye ba. Merkel ta bayyana matakan da za a dauka domin tunkarar "babban kalubalen" da Jamus ta fuskanta tun bayan yakin duniya na biyu.
Kokarin samar da rigakafi- Marylyn Addo
Mai bincike kan kwayoyin cututtuka, farfesa da ke jagorantar cibiyar bincike kan yaduwar cututtuka a cibiyar kula da lafiya ta Hamburg-Eppendorf, na aiki tukuru tare da tawagarta domin samar da rigakafin kwayar cutar coronavirus. Tuni ta samar da rigakafin cutar Ebola da kuma ta MERS coronavirus.
Matakan kariya- Jacinda Ardern
Karkashin Ardern New Zealand ta fara gwaji na bai daya tare da rufe kan iyakokinta, domin dakile yaduwar cutar. A ranar 14 ga watan Maris, Ardern ta umurci duk wanda ya shiga kasar, ya killace kansa na tsawon makonni biyu. A lokacin mutane shida ne ke dauke da cutar a kasar. Yayin da aka samu mutane 102 dauke da cutar ba tare da an rasa rai ba, ta hana baki shiga tare da killace kasar baki daya.
Gwajin coronavirus a kasa baki daya- Jung Eun-kyeong
An bayyana daraktar cibiyar binciken cututtuka da hana yaduwarsu ta Koriya ta Kudu, a matsayin "gwarzuwa ta kasa," kafofin yada labaran kasar sun bayyana cewa, ba ta bacci sosai kuma ba ta barin ofishinta, a kokarin yaki da annobar. Jung ta sa an dauki matakin yin gwajin coronavirus a kasar baki daya.
Share fage ga EU- Mette Frederiksen
A karkashin shugabancin Frederiksen Denmark ta zama guda daga cikin kasashen Turai na farko da suka dauki matakan dakile yaduwar coronavirus, ta hanyar daukar tsauraran matakai a rabin farko na watan Maris. Daga cikin matakan da ta dauka, kasar ta rufe baki dayan iyakokinta ga duk bakin da ba su da sahihiyar takardar izinin shiga kasar, wato bisa a ranar 14 ga watan Maris.
Matakin gaggawa- Tsai Ing-wen
Duk da kusancin da tsibirin ke da shi da makyankyasar kwayar cutar, Taiwan ta yi kokarin dakile matsalar. Gwamnatin Tsai ta dauki matakai cikin sauri domin hana hasashen kwararru na cewa Taiwan za ta kasance guda daga cikin inda annobar za ta fi bazuwa. An hana matafiya daga kasashen Chaina da Hong Kong da kuma Macau shiga kasar, tun bayan da adadin masu dauke da cutar a Chaina ya fara yawaita.