Najeriya: Mata na zanga-zangar neman hakki
March 2, 2022Kungiyoyin mata sun rinka rera takensu a fusace don nuna rashin yarda da abin da suka kira nuna son kai da ‘yan majalisa suka yi musu a lokacin gyaran fuska a tsarin mulkin Najeriya. Kudurori biyu ne dai 'yan majalisar suka yi watsi da su da suka shafi mata: Na farko shi ne wanda ya so ya sanya mata zama mataimaka a shugabancin jam'iyyu, da kuma kudurin da ya nemi ba su karin wakilci a takarar zama ‘yan majalisa.
Shin me ya yi zafi har ya kai ga fitowar mata?
Dr Jophia Gupar wacce ke daya daga shugabanin matan da ke zanga-zanga ta ce "Ba mu ga dalilin da zai sa majalisar dokoki ta Najeriya ta ki amincewa da abubuwan da mata ke so ba... Muna so suka sake duba abubuwan da mata suka ce a yi musu."
Matan sun shirya zaman dirshen a kofar shiga majalisar, lamarin da ya kawo cikas ga ayyukanta. Sai da a tilas aka rufe kofar majalisar a kan wannan batu na mata da ke daukar hankali a Najeriya. Niri Goyit da ke wakiltar kungiyar mata ta Women for Women da kuma Action Aid ta ce: "Aikin da ake yi ba mata, ba aiki mai kyau ba ne. Mu kuma ba mu da wata kasa baya ga Najeriya."
Majalisa ta kwantar wa matan da hankali
Mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar Sanata Robert Ajayi Boroffice ya jagoranci ‘yan majalisa don yi wa masu zanga zangar jawabi yana cewa: " Mun zo nan don mu saurare ku ta yadda za'a samu maslaha, ku sani matakin da aka dauka ba yana nufin wannan sashe da aka so yi wa gyara ba ya da muhimmanci ba ne."
Sai dai bayan wannan jawabi matan suka ce ba su fa yarda ba. Akwai dai matan da suka yiwo takakka daga yankunan Abujan a kan wannan batu irin su Safiyyah Tijjani. A bayyane take cewa matakin da ‘yan majalisar suka dauka ya yi wa matan Najeriyar zafi.