1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matan Saudiyya sun yi zabe

Yusuf BalaDecember 12, 2015

Kimanin maza 6,000 ne da mata 9,800 ke fafatawa a zabukan kananan hukumomi da ke cike da tarihi a kasar ta Saudiyya.

https://p.dw.com/p/1HMN3
Saudi-Arabien - Kandidatin für die Regionalwahlen
Aljazi al-Hussaini 'yar takara a zaben yankin Diriyah na Riyadh a SaudiyyaHoto: Getty Images/AFP/F. Nureldine

Dubban mata ne a kasar Saudiyya suka fita kada kuri'a a yayin da wasunsu ke zama 'yan takara cikin wannan zabe da ya kafa tarihi. Kimanin maza 6,000 ne da mata 9,800 ke fafatawa a zabukan kananan hukumomi.

Fiye da mata 130,000 ne suka yi rijista yayin da maza sama da miliyan daya da dubu dari uku suka yi rijistar. Hukumar da ke tsara zaben kasar ta Saudiyya ta bayyana cewa mutane miliyan biyar ne daga cikin miliyan 20 suka cancanci kada kuri'a. Sai dai ana ganin wannan adadi zai iya fin haka.

Nadiya Mohamad 'yar asalin kasar ta Saudiyya ta bayyana kada kuri'arta da wani " abin alfahari saboda irin ci gaban da aka samu a kasar Saudiyya, ina fatan yau za a zabi mace domin babbar dama ce ga 'yan uwana mata, wani abu da zai samar da sauyi a kasar".