1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lagos: Koyar da yara rawar Ballet

Abdullahi Tanko Bala
August 18, 2020

A jihar Legas da ke Najeriya, wani matashi Daniel Ajala wanda ya koyawa kansa rawa ta kafar intanet, ya bude makarantar rawa domin nuna wa matasa 'yan uwansa yadda za su nishadantar da kansu.

https://p.dw.com/p/3h9U9
Nigeria, Anthony Madu, Schüler der Leap of Dance Academy tanzt auf der Straße in Lagos
Hoto: Getty Images/AFP/B. Ibeabuchi

A jihar Legas da ke tarayar Najeriya wani mutum mai suna Daniel Ajala wanda ya koyar da kansa rawa ta kafar intanet, ya bude makaranta a tsakiyar unguwar talakawa domin koyar da rawar da nuna wa matasa 'yan uwansa yadda za su nishadantar da kansu.

A tsakiyar yankin d'Ajangbadi, da ke zama yanki da yawancin mazauna wurin talakawa ne, baya ga talauci rashin mazauni mai kyau da ma kayayakin more rayuwa kamar wutar lantarki da rashin hanyoyi masu kyau da kuma ruwan sha.

Duk da wannan bai sa Daniel Ajala ya yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ya nishadantar da kansa musamman ma idan a ka yi la'akari da hanyar da ya bi wajen koyon wannan rawar. Ajala dai na ganin rawar sai masu kudi ke yinta, ya ce ya yi hakan ne domin nuna wa jama’a cewa rashin kudi ba zai hana su more abin da ake yi a kasashen Turai ba.