Matasan Niger Delta sun ƙara yin garkuwa da ma´aikatan haƙo man Petur
October 10, 2006A yankin Niger Delta mai arzikin man petur, da ke kudancin Nigeria, matasa masu fafatakar ƙwato yancin yankin, sun ,kara garkuwa, da wasu ma´aikatan kampanin haƙƙo pan petur na Shell.
Sanarwar da hukumomin kampanin su ka hiddo, ta rataya alhakin wannan aika-aika, ga matasan ƙabilar Oporoma, a jihar Bayelsa.
Sanarwar ta Shell ta ƙara da cewa, ya zuwa babu wanda ya samu rauni, daga cikin ma´aikatan ta, da haɗarin ya rutsa da su, sannan hukumomin jihar, sun aika tawaga ta mussamman, domin tantanawa da shugabanin matasan.
A halin an rufe rijiyoyi da bututun mai na yankin da al´amarin ya wakana,hakan zai hadasa assara ganga 12.000 a ko wace rana.
A tsukin wattani 9 da su ka gabata an rufe riyiyoyi da dama a Niger Delta, a sakamakon tashe-tashen hankulla.
A satin da ya wuce, matasan sun kai irin wannan hari, a jihar Rivers, inda su ka kashe sojoji 14 na Nigeria, tare da yin awan gaba, da ma´aikatan mai 25, wanda har yanzu, babu ɗuriyar 7 daga cikin su.