HdM: Mai wakokin kare hakkin yara
May 13, 2020Matashiyar ta ce ta lura akwai iyayen yara mata da ke Tura 'ya'yansu zuwa kasashe da wasu garuruwan nenam kudi, ba tare da sanin irin hadarin da suke jefa yaran nasu ciki ba. Fatima ta nunar da cewa talauci da rashin ilimi na daga cikin abubuwan da ke sanya iyayen tafka wannan kuskuren. Ta ce ta bullo da hanyar amfani da wakokin zamani dan fargar da iyayen yara mazauna birane da karkara domin su daina tura 'ya'yansu a matsayin masu zuwa aikatau ko cirani a gidajen attajirai, inda a karshe ake lalata musu rayuwa.
'Yanci ga kanan yara
Fatima Ta kara da cewa wakarta na taimakawa wajan rage tauye hakkin yara da sauran ayyukan tallace-tallacen da suke zuwa cikin birane maimakon zuwa makaranta domin samun makoma mai kyau a rayuwa.
Akwai dimbin nasarorin da matashiyar ta samu tun lokacin da ta fara rera wakokin a faifan bidiyo da kuma yadde ake watsa shi ta kafafen sadarwa na zamani. Fatima ta bayar da tabbatacin cewa jama'a da dama ne ke karuwa da ire-iren wakokin da take rerawa wajan fadakar da al'umma.
Nasara tare da kalubale
Ta ce akwai mutane da yawa da suka kama sana'o'i duk sanadiyyar wakarta, yayin da wasu mata da ke bayar da 'ya'yansu zuwa birane suma suka fara tunanin canza ra'ayinsu. Daga cikin kalubalen da ta fuskanta akwai karancin kudin wallafa wakokinta da rashin samun taimako da kuma masu yi mata kallon tana yin wakokin ne domin cin mutuncin wasu.