1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mathai Wangari tayi tsokaci dangane da rikicin Kenya

MaidawaJanuary 22, 2008

Kokarin warware rikicin siyasa a Kenya da masu shiga tsakani

https://p.dw.com/p/Cw0s
Mai fafutukan kare hakkin jama'a da muhalli a Kenya,Wangari Maathai.Hoto: AP


Yan hasalin ƙasar Kenya mazauna ƙasar tare da al'aummar duniya suna kan cigaba da nuna damuwa dangane da yanayi tashe tashen hankula da suka addabi ƙasar halin yanzu, tun bayan zaben da akayi na ranar 27th, ga watan Dizambar shekara daga gabata.

Halin tashe tashen hankula da suka addabi kenya yanzu dai ya soma zama abin damuwa dake neman jefa yan hasalin ƙasar shiga halin ƙaƙanikayi, mussamam ma yan kenya dake ƙetare waɗɗan da suka taimaka gaya wajen gina ƙasar .

A can baya dai anyi ta ƙoƙari wajen shawo kan wannan rigima ta kenya, ta hanyar sasantawa to amma har kullum rikicin sai ƙara ta'azzara yake cikin salo daban daban.

yaau din nan ne ake sa ran cewar tsohon babban magatatarksar majalisar ɗinkin duniya Kofi Anan zai je kenya don buɗe wani

sabon babi a ƙoƙarin sassanta wato amma wacce alamu ke akwai na samun zarafin shawo kan wannan taƙƙadama ta siyasa ?

Parfessa Wangari Mathai wata fittaciyar yar siyasa ce yar ƙasar ƙenya, tayi tsokaci kan haka."Tace na tattauna da ɓangarorin biyu,kuma na roke su dasu yi la'akari da wahalhalu da alummomin wannan kasa suka faɗa da irin asarar rayuka da ake cigaba dayi,su warware wannan takaddama".

To dashike an kai ga wannan matsaya ko wace irin nasiha ke akwai ga shugabanin ganin cewar talakawa ne mussamam ma mata da yara ƙanana ke shigahalin ni yasu sanadiyyar wannan taƙƙadama,"Fatammun shine dukkannin ɓangarorin suyi la'akari da rayuwar alummarsu amma ba nasu bukatun kaɗai ba.Muna cigaba da kokarin ganin cimma madafa,kuma fatammu shine a samu nasa a yunkurin shiga tsakani daga ketare".

Ya zuwa yanzu da an ƙiyasta cewar fiye da mutane dubu 250 ne ke neman mafaka a kenya, yayinda wasu fiye da 700 suka riagamu gidan gaskiya, bayan halin ƙarancin abinci, da ruwan sha da sha'anin kiwon lafiya dake neman ƙara jefa jama'ar ƙasar shiga mawuyacin hali na rayuwa.