Matsalar man fetur a Najeriya
January 3, 2018Duk da cewa yanzu kamfanin man kasar na NNPC ya yi nasarar kai karshen matsalar a Legas da ke zama cibiya ta kasuwanci da Abuja babban birnin kasar ga dukkan alamu har yanzu da sauran aiki game da makomar harkar man fetur da al'ummar kasar ke dogaro a kai. Tashin farashin gangar danyen man ta sanya ba riba a tunanin manyan masu kasuwar kasar da ke cewar asara tai nisa ga batun shigo da man a kan farashin naira dari daya da saba'in da daya da ake sayar da shi akan naira dari da arba'in da biyar kan kowace lita yanzu.
Ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar ce kadai ke iya shigo da man dalilin da ya kai ga karancin hajjar a kasuwa kuma tuni aka shirya wani taro na masu ruwa da tsaki a cikin harkar da ya kunshi dilallan man ya zuwa jami'an tsaro har ma da masu sana'ar da jami'ai a masana'antar man kasar. An kwashi dogon lokaci ana tattaunawa da nufin neman mafitar matsalar.
Duk da cewar ana tsallen murnar samun kari na farashin danyan man fetur, batun shigo da tattacen na zaman babban rikici ga gwamnati da ke tsoron tunkarar al'umma ta kasar da batun yin karin. Tuni kungiyoyin kwadago suka gargadi gwamnatin kasar cewar ba su da shirin karbar duk wani kari na farashin da ke iya zaburar da su ya zuwa titi. Ko bayan nan yanayin siyasar da ya fara kadawa a kasar ya sa da kamar wuya mahukuntan kasar su dauki zabin karin da ke iya jawo matsala a tsakaninsu da 'yan zabe na kasar.