Kokarin shawo kan matsalar bakin haure a nahiyar Turai
August 21, 2015Talla
Kasashen dai sun amince da kafa sabuwar rundunar 'yan sanda ta hadin gwiwa domin dakile ayyukan masu safarar mutane da ke amfani da mashigar karkashin ruwa da ta hada kasashen biyu. Haka kuma sun kafa wani asusun hadin gwiwa na kudi kimanin Euro miliyan 10 a wani sabon yunkuri na kasar Birtaniya domin taimakawa masu neman mafaka da kuma mayar da wasunsu kasashensu na asali.
Rahotanni sun nunar da cewa sakatariyar harkokin cikin gida ta Birtaniya Theresa May da takwaranta ministan harkokin cikin gida na Faransa Bernard Cazeneuve ne suka bayyana sababbin matakan tsaron da suka dauka yayin ziyarar da suka kai mashigar karkashin ruwan da ta hada kasashen biyu a wannan Alhamis.