Sufuri ya samu cikas tsakanin Nijar da Mali da Burkina
October 19, 2021Matsalar tabarbarewar tsaron a tsakanin kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso ta soma tayar da hankalin direbobi da ma matafiya, kuma a cikin wannan yanayi shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya kai ziyara a kasar Burkina Faso, inda ya tattauna da takwaransa na kasar a kan hanyoyin tunkarar matsalar.
Duk da irin matakan da kasashen na Nijar da Mali da Burkina Faso ke dauka a kan yankin mai cike da hadari na kan iyakoki uku na kasashen nasu, kungiyoyin 'yan ta'adda da ma tsageru 'yan fashi da makami na ci gaba da gudanar da ayyukansu a yankin. Ko a karshen makon da ya gabata ma 'yan sandan Nijar uku sun halaka a kauyen Petelcole na kan iyaka da Burkina Faso, wanda ya fuskanci hari biyu a cikin kasa da awoyi 48. Kuma wani sabon salon da 'yan ta'addan suka fito da shi a wannan yankin shi ne na kai farmaki a kan motocin fasinja.
Malam Sa'idou Sonef direba ne da ke jigilar fasinja a tsakanin kasashen Nijar da Burkina da Mali, ya tabbatar da halin damuwa da suke gudanar da wannan sana'a tasu a tsakanin kasashen uku.
Ganin irin yadda wannan matsala ta tsaro ta zamo tamkar ana magani kai na kaba ta sanya shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya yi tafiya zuwa kasar ta Burkina Faso inda ya tattauna da takwaransa Roch Marc Christian Kabore kan hanyoyin gano bakin zaren warware matsalar kamar dai yadda ya yi bayani a taron manema labaran hadin gwiwa da suka yi a lokacin ziyarar.
"Kungiyoyin 'yan ta'adda sun zafafa ayyukansu a kan iyakokin kasashenmu guda biyu. Don haka ya zamo wajibi a gare mu mu dauki mataki na fuskantar matsalar. A ganawar da na yi da shugaba Kabore mun yanke shawarar kara hada karfi da karfe da yin aiki tare a fagen daga. Kazalika mun tattauna yadda ya kamata mu tunkari matsalar a fannin matakan soja da leken asiri da na shari'a. A takaice dai mun yi musayar bayanai masu muhimmanci, wadanda da za su taimaka wajen inganta shirinmu na tunkarar wannan kokowa da muke yi a tare."
Yanzu haka dai jama'a sun zura ido su ga tasirin da ganawar da shugabannin kasashen na Nijar da Burkina suka yi za ta yi wajen rage radadin wannan matsala ta tsaro a tsakanin kasashen nasu da sannu a hankali ta soma kawo cikas ga harkokin shigi da fice na kasashen.