Matsalar sa yara kanana a matsayin sojoji a yakin Siriya
December 31, 2013Wani mai magana da yawun hukumar kula da kananan yara ta MDD wato Unicef, ya ce binciken da hukumar ta gudanar ya kara tabbatar da rahoton da wata kungiyar kare hakkokin yara ta kasa da kasa da aka sani da Save the Children ta fitar, a cikin kwanakin da suka gabata. Kan cewa kungiyar Jabhatun-nusrah da ke da alaka da Alka'ida da kungiyar Da'ish mai fafutakar kafa gwamnatin Islama a kasar Iraki da Siriya, gami da kungiyar Liwa Abul fadlil Abbas, ta 'yan gani kashenin shugaba Bashar Assad, na daukar kananan yara a matsayin mayakansu.
A birnin Aleppo da 'yan tawaye ke rike da mafi yawansa, an bude wani sansanin bada horon yaran da ba su dara shekaru 16 da haifuwa ba. Kamar yadda wannan yaron yake tabbatarwa.
"Ni dan makarantar firamare ne, amma na jingine karatu, don na yi yakin taimakaon addinin Allah da kuma kare yara kanana 'yan uwana."
A sansanin Za'atar da ke kasar Jodan, ya kasance wani babban sansanin bada horo ga yara, kana da sojojin 'yan tawaye wadanda su ne suka ke kula da shi. Haka kuma yan tawayen ne suke bada yan kudaden masarufin da ba su taka kara sun karya ba ga yaran da ke karbar horon. Iyaye na tura yayansu don kwadayin yan kudaden da ake bawa yayan nasu.
"Shekaru na 15, na zo nanne don na koyi yadda ake harbi, don na je na yenta kasata daga sojojin mamaya na Iran da Hizbullah da kuma azzalimin shugaba Bashar."
Wani yaro da ke karbar maganin kaduwa a wata cibiyar magance matsalolin yaki ga yara kanana, da ke babban birnin kasar ta Siriya Demaskus, ya fadi irin tashin hankalin da ya gani;
"Baffana ne ya zo, ya ce min in biyo shi. Sai ya kawo ni wurin wasu sojoji biyu daure, kana ya bani adda yace in sare kawunansu."
Amfani da kafofin sadarwa na zamani da mayakan sa kan ke yi wajen ingiza yara, kana daukar makamai don yin yaki, na kara bazuwar matsalar da kara mata sarkakiya. Kamar yadda wannan faifayin bidiyon ke nuna wani yaro, dan shekaru bakwai dauke da jigidar alburusai, ta bindiga mai sarrafa kanta.
"Ina kira ga dukkan musulmin duniya da su ankara, su dau makamai don yin jihadi kan shugaban kama karya na kasar Sham."
Kamar dai yadda alkaluman da kungiyoyi masu fafutuka ke nuni, fiye da yara kanana dubu 11 suka mutu, sakamakon rowan bama-bamai ta sama da yawancin sojojin gwamnatin Siriya ke kaiwa. Inda dubbai daga yara kananan suka jikkata, ko suka rasa yan uwa. Al'amarin dake kara barazanar tsundumarsu cikin yaki, da zimmar daukar fansa ko don ta more.
Mawallafi: Mahmud Yaya Azare
Edita: Usman Shehu Usman