Sakkwato: Matsalolin 'yan gudun hijira
May 9, 2023Wata mata Hadiza da ke gudun hijira a sansanin unguwar Lowcost a birnin Sakkwato, ta yi korafi tare da bayyana irin halin da rayuwarsu ta kasance sakamakon karancin abincin da suke fuskanta. 'Yan gudun hijirar dai sun ce irin yanayin rashin da kuma karancin abinci da suke fama da shi, ya sa ba su da wani zabi face su fita neman abun da za su ci su kuma ciyar da 'ya'yansu. Koda yake 'yan gudun hijirar sun nuna yadda wasu ke zuwa suna daukar hotonsu tare da su, sai dai kuma suna arzita kansu ne da abincin da aka ma kayan tallafin da aka tara dominsu.
Sai dai a wasu lokuta ana samun kungiyoyi masu tallafawa tare da taimakon 'yan gudun hijirar. Wani dattijo Isiyaka da ya baro gidansa a yankin gabashin Sakkwato sakamakon aika-aikar 'yan bindiga, ya ce har yanzu bai yanke kauna ga komawa gida ba. Sauyin shugabanci da aka samu a Najeriyar ya sa tuni 'yan gudun hijirar sun fara fatan a samu isashen tsaro, domin su koma gidajensu su ci gaba da rayuwarsu ta yau da kullum.