Matsayin matan Kenya a zaɓe mai zuwa
February 12, 2013Zaɓen ƙasar kenya da zai guda a watan gobe dai, tamkar wani sabon juyin juya haline a ƙasar, inda ake fatan samun sabbin tsari na tafiyar da ƙasar, misali tuni aka ware wa mata kaso na musamman a kujerun majalisar dokokin ƙasar.
Wannan yana daga cikin abinda sabon kundin tsarin mulkin ƙasar ya nada, kuma ko da a yaƙin neman zaɓe da ake yi, batun na mata yana ɗaukar hankali. Inda yanzu aka ware ɗaya bisa uku na yawan kujerun majalisar ga mata. A da mata ba su da wani tasiri a siyasar ƙasar.
Damar samun mace shugabar ƙasa dai kusan tini ya kau, domin alƙaluman ra'ayoyin jama'a da aka fitar, ya nun cewa Martha Karuwa wanda itace mace yar takkaran shugaban ƙasa, tana da wuyan samu nasara. Aksarin siyasa a ƙasar Kenya maza ne ke kankane shi.
To amma fa dole yanzu kam a samu sauyi, domin sabon kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadi a baiwa mata klashi ɗaya bisa uku na dukka wasu guraben siyasa, don haka babu inda maza kadai za su wawure komai. Rachel Yegon tana daga cikin yan takaran majalisar dokoki. Ita dai bata matsalar kudi kamar sautran mata Kenya domin yar kasuwace
Matsalolin Matan Kenya
Wannan shine babbar matsalar matan kenya, nmata basu kuɗi, ba a tallafa musu. Idan mace tana son tsayawa takara dole sai ta samu izinin mijinta, sai ta roƙe shi ya bata motar da za ta yi yaƙin neman zaɓe, dole komi ko da yaishe sai kana tambayarsa, harma ya gaji da ke, don hanka ba zai bakiƙwarin gwiwa ki yi siyasar ba"
A ƙasa kamar Kenya dai ayan siyasa na buƙatar kuɗi, kama da daga buga posta, da yaƙin neman zaɓe, da rijista a jam'iya, ga kuma baiwa su kansu masu zaɓen kuɗi. Wasu matsalolin da masu lura da siyasar Kenya ke bayyana shine, matan ƙasar basu zurfin ilimi, wanda shine ake buƙata ƙasar Kenya, don haka wasu wuraren a dole suke baiwa maza fili.
Su kansu wadanda suka rubuta sabuwar dokar zaben sun kwana da sanin wannan matsalar, don haka suka baiwa mata kujeru 47 daga cikin kujeru 222 na majalisar dokokin ƙasar. Hassane Umar ɗan takarn majalisar dattawann ƙasar ne Mombasa
"Abun yana damuna yadda mata ke samun koma baya,misali mun ware ko wace matsaba a fidda mace guda, amma abun kaito shine a wasu wurare suna ɗari-ɗarin fitowa, hakan ya sa suna rasa wata babbar dama"
Ko da itama Rachel Yegon yar takarar majalisar dokoki, ta bayyana cewa gogayya da matasa a yaƙin neman zaɓen jan aiki ne.
Abinda zan faɗa shine, al'ada ta mai da mata baya, kuma a zahiri mata sune dukkan aikin cikin gida suna kula da iyali, har sai yara sun girma sun fara zuwa makarata su fahimci haölinda ake ci"
Fatan masana a siyasar ƙasar kenya dai shine, a samu matan su kawo takaita babbancin ƙabila da ake fiskanta, saɓanin maza da a yanzu suka fi fifita dangensu, jmusamman idan suna neman matan aure. Wannan shine ake ganin mata za su iya tallafawa, inda za su kawar da ƙabilanci su rungumi siyasa dake gabansu.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Moohamadou Awal Balarabe