Ana ci gaba mallakar bayi a Mauritaniya
March 17, 2020Wani dan fafutuka Baliou Coulibaly ya yi bayanin yadda ake bautar da mutane a matsayin bayi a Mauritaniya. A yayin wani balaguron da yayi ya nuna wa 'yan jarida wasu matasa da ke wasu 'yan ayyukan da ke tabbatar da tabi'ar bautar. Sai dai ya koka da yadda ba a bari matasan su yi magana da bakuwar fuska domin ubangidansu bai ba su damar yin haka ba. Kuma suna tsare wannan umarni koda kuwa ubangidan nasu ba ya kusa.
Duk da haka an samu zantawa da wani mai suna Matala Ould Mboirik wanda a yanzu ya samu 'yanci bayan ya dandana kangin bauta a shekarun baya inda ya bayyana cewa:
''Na taso a cikin bauta amma ban taba yarda da wannan harka ba don na san cewa ba abu ne mai kyau ba. A duk lokacin da na yi yunkurin tserewa daga wurin ubangidana sai in tuna cewa wannan abu ne mai hadari, domin idan har aka kamo ni za a iya kashe ni domin ni na ga wadanda suka yi yunkurin tserewa aka kuma kamo su aka kashe su."
A lokacin da Matala yake rayuwa a matsayin bawa, ayyukansa sun hada da kula da shanu da rakumma da kuma hura wa mai gidan shi wuta ta jin dimi. Sai dai bai san shekarunsa na haihuwa ba, amma yana iya tuna cewa ya samu 'yanci a shekara ta 2003, kuma a duk lokacin da ya tuna rayuwar bautar da ya yi ransa na baci kwarai. A yanzu yana da mata biyu da 'ya'ya biyu.
Kungiyar kare 'yancin dan Adam kan bauta a Mauritaniya
Joumoua Ould Meissara shugaban wata kungiyar kare 'yancin dan Adam ne a kasar Mauritaniya yana yi wa kansa inkiya da sunan dan Afirka bakar-fata. Kuma a cewarsa galibin wadanda ake mayarwa bayi a Mauritaniya bakaken fata ne. Ya yi zargin cewa Larabawa fararen fata 'yan Afirka sune ke azabbatar da mutanen a matsayin bayi. Ya kuma zargi gwamnati da kawar da kanta a kan wannan matsala.
A shekara ta 1981 Mauritaniya ta zama kasa ta karshe a duniya da ta haramta cinikin bayi. Sai dai kawo yanzu babu wasu dokoki masu tsauri da aka tanadi wurin hukunta masu aikata wannan dabi'a. A shekara ta 2007 da Mauritaniya ta ga kasashen duniya sun sa mata ido, sai ta ce za ta fara aiwatar da hukunci. Amma har yanzu ana zargin manyan 'yan siyasa da a yanzu haka ke da wasu bayi a gidajensu, da hana ruwa gudu wurin aiwatar da dokokin.