Mawakan Watoto na tashe a duniya
April 20, 2016Mawakan Watoto wani rashe ne na mawakan majami'ar Watoto Pentecostal a birnin Kampala na Yuganda, Watoto dai a harshen Swahili na mai ma'anar kananan yara, mawakan dai na baje kolinsu a Afirka da Turai da Kudancin Amirka gami da nahiyar Asiya kuma sun shafe shekaru goma suna wadannan wake-waken.
Yaran da ke cunkushe a wata barandar makarantar kasa da kasa ta Bonn a yayin da suke shaukin fara wake-wakensu a gaban Jamusawa masu sha'awar wakokinsu.
Yaran dai da shekarunsu sun tasarma shida zuwa 13 sun yi ado da wasu kaya masu launin kaloli da takalma, jim kadan da bude kofar farfajiyar wajen waken sai yaran da suka tasarma 18 suka fara abin da ya kawo su na kade-kade da raye-raye.
Roy Kaddu shi ne jagoran tawagar yaran ya yi mana karin haske akan wakokin:
"Tun a shekara ta 1994 majami'ar Watoto take aikewa da yaran makaranta domin nakaltar wakoki kamar wannan, domin zayyana hikayar Annabi Isa da tarinhinmu gami da fadakarwa akan makomar yaran Afirka, abin da ya sanya wannan ya zama na daban shi ne kowacce shekara mu kan fita da yara daban-daban. A kwai dai damarmaki da yawa ga yaran muddin suka fita duniya tare zama gogaggu.
Gary Skinner da ke zama malamin majami'a dan asalin kasar Kanada shi ne ya kirkiro da Watoto a shekara ta 1994, kuma mujami'ar ta ci gaba da kulawa da kananan yaran da suka rasa iyaye ko 'yan uwansu sakamakon yaki ko kuma cutar HIV ko Sida, wannan dai wata yariya ce wacce ke cikin tawagar Watoto.
"Sunana Patience kuma shekaruna 10 da haihuwa, ina matukar son a dama da ni a cikin tawagar Watoto, sabili da zai taimaka maka sanin Allah tare da jima wasu yadda mahalici yake".
Masu daukar nauyin wake-waken da kuma masu fatan alheri na taka muhimiyar rawa wajen tallafa wa kananan yaran da ake reno a majami'ar. A yayin da a karshen wake-waken mahalarta gangamin kan cika da mamakin irin yadda yaran kan rera wakokinsu.