May: Muna bukatar hadin hadi kai da Amirka
January 27, 2017Talla
Firaministar Birtaniya Theresa May ta isa kasar Amirka domin ganawa da shugaba Donald Trump. Ziyarar da ke zama ta farko da shugaban na Amirka zai gana da wani shugaba na kasar waje.
Da ta ke jawabi ga taron shekara shekara na sanin makama kan manufofi na yan jam'Iyyar Republican a birnin Philadelphia, Theresa May ta nuni ga karkata akalar manufofinta na ketare tana mai baiyana matsayi daidai da na Trump.
Tana mai kira ga kasashensu biyu su hada kai domin tunkarar sabbin kalubale.
Ko da yake kasashen biyu na Amirka da Birtaniya su na da danganataka ta musamman a tsakanin su ziyarar na zama zakaran gwajin dafi a yadda manufar Trump z ata kasashe a danganataka da kasashen Turai.