May na son a takawa Koriya ta Arewa birki
August 30, 2017Talla
Firaminista May ta ce China na da rawar da za ta taka sosai wajen ganin an warware wannan batu na gwaje-gwajen makaman da Arewan ke yi wanda hakan inji ta ka iya tunzura wasu kasashen duniya. Wannan kira na May dai ta yi shi ne lokacin da ta ke kan hanyarta ta zuwa kasar Japan domin tattaunawa da Firaministan kasar Shinzo Abe. Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da mahukuntan Pyongyang suka yi wani gwaji na makami mai linzami wanda ya ratsa ta cikin Japan kana ya fada cikin Tekun Pacific.