1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan IS sun halaka dakarun Najeriya

Yusuf Bala Nayaya MNA
January 28, 2019

A wani sako da mayakan na IS suka fitar ga kafar yada labarai a ranar Lahadi sun ce suna da hannu a kai harin Lomani.

https://p.dw.com/p/3CIVA
Kamerun Symbolbild Soldaten im Norden ARCHIV
Hoto: Getty Images/AFP/R. Kaze

Mayakan IS sun bayyana cewa sun halaka dakarun sojan Najeriya 30 a wani hari da suka kai a ranar Asabar a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, ikirarin da dakarun sojan na Najeriya suka karyata.

A cewar mai magana da yawun dakarun sojan na Najeriya harin da aka kai kan sojan kasar a kauyen Logomani a ranar Asabar dakarun sun kori mayakan na Boko Haram sai dai sojoji takwas sun samu raunika, babu kuma wani rauni da ke zama barazana ga rayuwar wani daga cikin sojojin.

A wani sako da mayakan na IS suka fitar ga kafar yada labarai a ranar Lahadi sun ce su ke da alhaki na kai harin da aka kai a Lomani. Mayakan na IS dai reshen Afirka ta Yamma (ISWA), wadanda suka raba Boko Haram gida biyu a 2016 sun kai hare-hare a watannin baya-bayan nan a Arewa maso Gabashin Najeriya.