Afirka ta Kudu na mayar da bakin haure
May 14, 2020Da ma dai sun jima suna tsare a hannun mahukunta, a wata cibiya da ake kira Lindela Repatriation Centre da ake ajiye mutanen da hukumomi a Afirka ta Kudun ke son mayarwa kasashensu na asali. Sai dai kuma bullar cutar coronavirus ta sanya hukumomi hanzarta mayar da su kasashen nasu. Na baya-bayan da suka isa kasarsu sune 'yan kasar Zimbabuwe da aka zuba su cikin motocin safa-safa zuwa kasarsu. Siya Qoza shi ne ke magana da yawun ministan harkokin cikin gida na Afirka ta Kudun, ya kuma kare matakin da gwamantin nasu ke dauka, inda ya ce duk wanda aka mayar watakila yana zaune a kasar ne ba bisa ka'ida ba. Bayan 'yan Zimbabuwe akwai 'yan kasar Lesotho guda 94 da su ma aka mayar da su daga Afirka ta Kudun.
Kafin a mayar da su kasarsu, an zarge su da kitsa wata zanga-zanga a cibiyar da aka ajiyesu, inda a sakamakon haka wasu daga cikinsu suka tsere daga hannun mahukuntan. A saboda haka aka tarkata su su kusan 400 aka mika su kasar Mozambik. To sai dai Ngqabutho Mabhena shugaban 'yan Zimbabuwe mazauna Afirka ta Kudu na ganin matakin bai dace ba. ''Ya kamata ace an duba 'yan uwantaka, mu dukkanmu 'yan Afirka ne. Mu muna ganin ya kamata a dakatar da mayar da mutane kasashensu a wannan lokaci na COVID-19, domin idan ka kama mutane ka mayar da su kasarsu, kana bayar da hurumin yaduwar cutar a kasashe makwabta ke nan.''
To amma duk da haka, ma'aikatar kasashen waje ta Afirka ta Kudun ta shaidawa 'yan majalisar kasar cewa, nan ba da jimawa ba za ta mayar da 'yan kasar Malawi su wurin 500 da ke hannunta zuwa kasarsu.