1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta bukaci adalci a rabon allurar Corona

Gazali Abdou Tasawa
April 21, 2020

Kasashen 193 mambobin MDD sun kada kuri'ar amincewa da wani kudirin doka wanda ya tanadi tabbatar da adalci a tsakanin kasashen duniya wajen rarraba allurar Coronavirus wacce ake sa ran kirkirowa a nan gaba.

https://p.dw.com/p/3bEIk
UN Generalversammlung Rede Kim Song
Hoto: picture-alliance/AP Photo/R. Drew

Kasashen 193 mambobin Majalisar Dinkin Duniya a wannan litinin sun kada a  kuri'ar amincewa da wani kudirin doka wanda ya tanadi tabbatar da adalci a tsakanin kasashen duniya wajen rarraba allurar rigakafin cutar Coronavirus wacce ake sa ran kirkirowa a nan gaba.

Wasu jami'an diplomasiyya da suka bukaci a sakaya sunansu sun kwarmata wa kamfaninin dillancin Labaran Faransa na AFP cewa Amirka ta yi yunkurin hawa kujerar naki domin hana daukar kudirin amma abin ya ci tura.

Daga karshe dai ta ba da kai bori ya hau, lamarin da ya sa kudirin wanda kasar Mexico ce ta shigar da shi a gaban Majalisar Dinkin Duniya ya samu goyon bayan illahirin kasashen 193 mambobin majalisar. Manyan likitoci a kasashen duniya dabam-daban ne dai suka dukufa yanzu haka wajen samo allurar rigakafin cutar ta Coronavirus wacce ake fargabar manyan kasashen duniya su yi kaka gida a kanta.

Zuwa yammacin wannan Talatar dai alkaluma sun nunar da cewa mutane sama da miliyan biyu da rabi ne suka harbu da kwayoyin cutar a duniya, kuma ta halaka mutane kusan dubu 172, amma kuma wasu mutanen kusan dubu 660 da suka kamu da cutar sun warke.