1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Rayuwar 'yan cirani na salwanta wajen tsallaka teku

Abdourahamane Hassane
November 15, 2019

A rahoton da ta bayyana hukumar kaura ta Majalisar Dinkin Duniya OIM ta ce rayuwar 'yan cirani da bakin haure na salwanta a kowace shekara a lokacin da suke kokarin tsallaka tekun Mediterranean.

https://p.dw.com/p/3T7Bx
Libyen Gerettete Flüchtlinge in Tripolis
Hoto: Getty Images/AFP/M. Turkia

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tun daga shekara ta 2014 sama da bakin haure da 'yan cirani dubu 19 suka mutu ko suka bata a lokacin da suke kokarin tsallaka tekun Mediterranean ta jiragen ruwa marasa inganci. Kakakin hukumar kaura na Majalisar Dinkin Duniya  OIM Joel Millman wanda shi ne ya bayyana wannan sanarwa. Ya ce a wannan shekara kimanin bakin haure dubu 92 suka tsallaka tekun zuwa nahiyar Turai galibi kuma sun iso  ta Girka inda aka yi rijistar mutane dubu 50 sai Spain da dubu 22.