1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muradun karni na 2030 a Afirka da ci gaban kasashe

Salissou Boukari
July 25, 2024

Mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed, na ziyarar aiki a wasu kasashen yammacin Afirka domin tattaunawa da shugabannin kan muradun karni na 2030 da batun ci gaban kasashe

https://p.dw.com/p/4ik7O
Äthiopien UN-Untergeneralsekretärin Amina Mohammed in Addis Abeba
Hoto: Solomon Muchie/DW

Mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya ta gana da Firaministan Nijar kafin daga bisani ta gana da shugaban kasar Birgediya Janar Abdourahamane Tiani. Amina Mohammed ta somo wannan ziyar ce ta kasashen yammacin Afirka daga birnin Dakar na kasar Senegal zuwa Guinea, Mali, sannan ta koma kasar Habasha, inda ta halarci wani taro kan batun samar da kudaden raya kasashe inda daga bisani ta dawo kan hanyarta zuwa Burkina Faso sannan ta isa Nijar.

Amina Mohammed mataimakiyar sakataren MDD
Amina Mohammed mataimakiyar sakataren MDDHoto: Luiz Rampelotto/ZUMA Wire/IMAGO

Mataimakiyar Sakatare-Janar din ta gana da manyan jami'an gwamnati, da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da ke kasashen da sauran masu ruwa da tsaki, domin yin nazari kan kalubalen da ke kawo cikas wajen cimma muradun karni da irin goyon bayan da MDD za ta bayar don cimma wadannan muradu ta yadda al'umma za ta gani a kasa. Amina Mohammed ta jaddada muhimmancin wannan ziyara.

"Na farko dai muna da tarin matsaloli na tashe-tashen hankula da yake-yake a wadannan yankuna, ga sauye sauyen mulki da aka fuskanta daga farar hula zuwa na sojoji ga matsalar sauyin yanayi ga kalubalen agajin gaggawa ga wadanda suka bar matsuggunan su. Ta haka ne muke tattaunawa da magabata da sauran wadanda abun ya shafa domin samun hanyoyi mafita dole ne a ciga da ayyukan raya kasa don cimma burin da aka sa a gaba na muradun karni a dukannin yammacin Afirka.”

Amina Mohammed mataimakiyar sakataren MDD
Amina Mohammed mataimakiyar sakataren MDDHoto: picture-alliance/EuropaNewswire/L. Rampelotto

Wadannan manufofi wani mataki ne na dorawa kan kokarin da mataimakin babban sakataren MDD mai kula da ayyukan raya yankin Sahel, da na daraktan yankin Afirka suka yi a kasashen lokacin da suka jagoranci wata babbar tawaga zuwa Nijar a watan Yuni da ya gabata.Inda mataimakiyar sakataran na MDD ta tabo batutuwan tsaro da ke kawo cikas a fannin cigaba.

"Batun tsaro na daga cikin babban batu mai mahimmanci ga wadannan kasashe baki daya kuma shi ne 'yanci na farko na al'umma don haka batu ne da ya shafemu mu duka domin ga dukannin jagororin da muka tattauna da su yayin wannan ziyara, batun tsaro shi ne a sahun gaba na kalubale  da kuma yadda kowa ke da bukatar ganin an samu magance matsalar don samun zaman lafiya mai dorewa wanda sai da shi ne ake iya samun ci gaba. Sannan batun yan gudun hira na ciki da na waje batu ne mai sarkakiya domin adadin yan gudun hijirar da kuka bai wa mafaka a nan na wani matsin kaimi a fannin ilimi, da kiwon lafiya da batun samun abinci.”

Wau al'ummar Nijar magoya bayan shugaban kasa Tiani
Wau al'ummar Nijar magoya bayan shugaban kasa TianiHoto: AFP/Getty Images

Mataimakiyar Sakatare Janar na MDD ta kara da cewa lalle ne duk irin gudunmawar da MDD za ta kawo a wadannan fannoni za ta dace ne da burin da gwamnatin Nijar ta sa wa gaba inda ta ce ta tattauna da walillansu da ke nan Nijar da kuma wakilin bankin Duniya da dukanninsu za a karkata ayyukan daidai da bukatun da gwamnati ta sa wa gaba don ci gaban al'umma. Kuma daga nasu bangare hukumomin Nijar sun yaba wannan ziyara inda suka yi wa mataimakiyar sakatare Janar din kyaukyawan tarbo na nuna farin cikin wannan ziyara wanda suka ce za ta taimaka wajen zaburar da ayyuka da dama na ci gaban al'umma.