MDD ta bukaci a fara tallafawa kasashe matalauta
March 5, 2023Talla
A zauren taron kasashen duniya da aka barsu a baya a fannin ci gaba da ke gudanaa birnin Doha na Qatar, ya bukaci kasashe masu karfin tattalin arziki da su dinga bawa kasashe matalauta tallafi domin kaucewa yawan cin bashi da suke yi.
Hukumar ta UNDP ta ce daga cikin kasashe 52 akwai kasashe 25 da ke kashe sama da kaso biyar na kudaden shigarsu wajen biyan bashi, lamarin da hukumar ke cewa ba shi ne mafita ba.
Daga cikin kasashen da ake kokarin samar wa mafita daga basussuka, 23 na yankin kudu da hamada sahara, kuma kasashen irinsu Najeriya da Mali da Burkina Faso sun lalata sama da shekaru 20 na ci gaba saboda rigingimu da ke da nasaba da siyasa da gazawar gwamanti na samar da ababen more rayuwa.