MDD ta bukaci Jammeh ya bada hadin kai
December 13, 2016Talla
Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh ya gana da tawagar masu shiga tsakani daga kasashen duniya wadanda suka tashi zuwa Banjul domin rarrashinsa ya mika ragamar mulki.
Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari da shugabar Liberia Ellen Johnson Sirleaf da shugabannin Saliyo da na Ghana da kuma manzon Majalisar Dinkin Duniya a yammacin Afirka Muhammed Ibn Chambers za su sauka birnin banjul a yau Talata domin ganawa da shugaban.
Kwamitin sulhun Majalisar ya bukaci shugaba Jammeh ya bada hadin kai ga tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya da ta kungiyar raya ci gaban kasashen yammacin Afirka ECOWAS domin cimma masalaha cikin ruwan sanyi.