1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

MDD ta damu a game da sabbin dokokin da'a a Afganistan

Binta Aliyu Zurmi
August 25, 2024

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ke Afganistan, ta nuna damuwarta matuka a kan sabbin dokokin da'a da gwamnatin Taliban ta fidda a kasar.

https://p.dw.com/p/4jtmM
Afghanistan Taliban feiern Jahrestag Machtübernahme
Hoto: Siddiqullah Alizai/AP/picture alliance


Sabbin dokokin da tawagar ta ce takunkumai ne aka sanya a kan mata, wanda kuma take ganin ka iya zama koma baya ga harkokin rayuwarsu ta yau da kullum da ma yancinsu.

A ranar Larabar da ta gabata ce hukumomin Taliban suka fidda dokokin da suka yi bayani a kan salon rayuwa, wanda kuma ake yi wa fasarar tsauraran shari'ar Musulunci.

Dokokin sun tanadi hukunce-hukunce masu tsauri ga duk wanda aka kama da laifin karyasu. Dokoki da dama a Afganistan sun hana mata zuwa makaranta da yin aiki har ma da  ziyarar shagunan gyaran jiki.