1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

MDD ta yi tir da harin Isra'ila a shalkwatar Lebanon

Binta Aliyu Zurmi
October 10, 2024

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da ke Lebanon, ta ce dakarun Isra'ila sun kai hari a shalkwatarsu da ke kudancin kasar, harin da ya yi sanadiyar jikkata wasu mambobinta.

https://p.dw.com/p/4leQr
Libanon, Khiam | UN-Friedenstruppen im Grenzgebiet zu Israel
Hoto: Aziz Taher /REUTERS

Tawagar ta UNIFIL mai akalla sojoji dubu 10 a kudancin kasar ta zargi sojojin IDF da kai mata hare-hare tun bayan gargadinsu na su fice daga yankin kudancin Lebanon da suka yi.

Tuni ministocin tsaron kasashen Italiya da Indonesiya da ke da mafi yawan sojiji a tawagar, suka kira jakadojin Isra'ila da ke kasashensu domin bayar da ba'asi a kan harin da ya jikkata dakarunsu.

Wannan harin dai shi ne na baya-bayan nan da ya rutsa da maboyar karkashin kasa da dakarun na Majalisar Dinkin Duniya ke samun mafaka. 

 

Karin Bayani:Yara na kwana a kan titunan Beirut sakamakon rikici