Ba adalci ba ne a sake gudanar da sabon Zabe
November 25, 2017Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na shirin amincewa da kafa gwamnatin hadin gwiwa da Jam'iyyar Social Demokrats SPD. Jam'Iyyar ta SPD ta ce za ta gabatar da sharuda a tattaunawar ta hadakar manyan jam'iyyu don kafa gwamnatin gambiza. Shugabar gwamnatin dai ta baiyana a taron jam'iyyarta cewa bai dace a sake kiran jama'a su fito domin sake kada kuri'a ba.
Shugabar gwamnatin Angela Merkel ta sauko daga matsayin da ta baiyana a farko game da zaben.
Da take jawabi ga taron jam'iyyarta ta CDU a Jihar Mecklenburg-Pormerania, Merkel ta ce wajibi ne Jamus ta sami gwamnati mai dorewa da zaman lafiya wadda kuma za ta ciyar da kasar gaba tana mai cewa kuskure ne a ce za a sake bukatar jama'ar kasa su fito domin wani sabon zabe.
"Jama'a sun yi zabe, idan ba za mu iya yin wani abu akan sakamakon ba, to kuwa bai kamata a ce za mu sake kiran jama'a su fito domin sake kada kuri'a ba. Wannan ba hurumin mu ba ne, ya rage ga shugaban kasa ya yanke hukuncin abin da za a yi. To amma a matsayin mu na 'yan siyasa da muka sami amincewar al'ummar mu, sake kira su fito wani sabon zabe abu ne da nake gani bai dace ba."
Kasar ta Jamus dai ta shiga yanayi mawuyaci kuma mai sarkakiya irin wanda ba a taba gani ba tsawon shekaru da dama, bayan da a makon da ya gabata aka kasa cimma daidaito a tattaunawar kafa gwamnatin hadin gambiza tasakanin jam'iyyun CDU da Green mai rajin kare muhalli da kuma FDP mai muradin cigaban kasuwanci.
Shugaban jam'iyyar Christian Lindner ya maida martani kan sukar da ake yiwa jam'iyyar cewa ita ce ta kawo cikas.
"Na lura da sukar lamiri da ake yi wa FDP, to amma ina gani batu ne na kare hakkin da ka dauka na siyasa ba wai ka mika wuya ga kowace irin masalaha ba. Idan muka ce mun amince, to gwamnatin hadakar da za a kafa ba za ta yi karko fiye da shekaru hudu ba."
A dai sakamakon koma bayan da Jam'iyyar Merkel ta samu a babban zaben gama gari da ya gudana a watan Satumba da kuma kin amincewar jam'iyyar SPD na shiga babban kawancen gwamnati da jam'iyyar CDU ta Merkel, ya sa jam'iyyar ta CDU ta nemi yin kawance da kananan jam'iyyu domin kafa gwamnati. Sai dai kuma bayan da jam'iyyar FDP ta janye daga tattaunawar bisa sabanin akida, wannan matsayi ya jefa shugabar ta Jamus wadda ta dade a karagar mulki, cikin wadi na tsaka mai wuya watanni biyu bayan zabe ba tare da kafa gwamnati ba.
A kan haka ne a makon da ya gabata, Merkel ta ce a shirye take ta shiga sabon sabon zabe maimakon kafa gwamnati mara rinjaye. To sai dai a ranar Asabar ta sauya matsayi inda ta ce ba adalci ba ne a ce za a kira sabon zabe.
Mai yiwuwa dai karfin gwiwar da Merkel ta samu cewa za a iya cimma nasarar kafa gwamnatin kawance, baya rasa nasaba da sassautowar da ita ma jam'iyyar SPD ta yi wadda da farko ta ce ba za ta shiga kawancen gwamnati da jam'iyyar Merkel ba.
Sai dai yayin da ake cigaba da kiki-kaka lamarin ya fara harzuka masu zabe. Wannan ya sa a ranar Juma'ar da ta wuce shugaban jam'iyyar SPD Martin Schulz ya ce zai kauce wa matakin faranta wa jam'iyya ya nemi ra'ayin jama'a ko suna bukatar a shiga kawancen gwamnatin ko kuma a'a.
"Cikin kwanaki da makonni masu zuwa, za a yi tattaunawa da dama, za mu tattauna sosai a kan kowane bijire, a mataki na shugabancin jam'iyya da kuma kungiya ta 'yan majalisar dokoki. Abu guda da ke a baiyane shi ne shin tattaunawar za ta kai mu ga shiga gwamnati? 'Yan jam'iyya su za su yanke hukunci."
A yanzu dai jama'ar Jamus za su ci gaba da jira na wani lokaci kafin su ga kafa sabuwar gwamnati.