Merkel da Schulz sun kada kuri'unsu a zaben Jamus
September 24, 2017Merkel dai ta kada kuri'arta ce a birnin Berlin da ke gabashin kasar yayin da Schulz ya yi nasa zaben a garinsu na Würselen da ke yammacin Jamus. Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi kira ga al'ummar kasar da su fita kada kuri'a a zaben na 'yan majalisa a wannan rana ta Lahadi. A wani gajeran jawabi da ya yi, shugaban ya ce hakki ne na duk wanda ya cancanci zabe ya fita ya kada kuri'arsa.
Tun da misalin karfe 8 na safe agogon Jamus ne aka bude tashoshin kada kuri'a bisa matakai na tsaro musamman a Berlin kuma za a rufe rumfunan ne da karfe 6 na maraice inda kai tsaye za a fidda sakamakon farko na zaben. Shi dai wannan zabe wani mataki ne girka gwamnati inda jam'iyyar da ke da ke kan gaba za ta nemi wadda za ta yi da ita don kafa gwamnati.