Merkel: Waiwayen baya da tsokaci kan Putin da Trump
November 21, 2024Tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta baiyana yadda dangantakarta ta kasance tsakaninta da shugabannin duniya kamar shugaban Rasha Vladimir Putin da Donald Trump a zamanin mulkinta na shekaru 16 a littafin da ta rubuta na waiwayen baya yayin da ta ke shan suka cewa ita ce ummul haba'isin rikicin da ake fama da shi a yanzu.
A ta'alikin da aka fitar gabanin kaddamar da littafin wanda za a yi a ranar 26 ga watan Nuwamba, Merkel ta tabbatar da kudirinta na kin amincewa Ukraine zama mamba a kungiyar kawancen tsaro ta NATO a taron kolin kungiyar da aka yi a 2008 a Bucharest wanda manazarta suka ce mai yiwuwa hakan shi ya hana Rasha kai wa Ukraine mamaya a wancan lokaci.
Littafin na tarihin Merkel ya kuma nuna yadda ta nemi bai wa Paparoma shawara kan yadda zai yi mu'amala da Trump lokacin da aka zabe shi karon farko a matsayin shugaban Amurka, inda ta yi fatan shawo kan mutumin da ta lura yana da halayyar ya samu ko kuma a fasa kowa ya rasa, tare da kokarin jan hankalinsa ka da ya janye daga yarjejeniyar sauyin muhalli da aka cimma a Paris.