1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mexico: An gano gawarwakin mutane 166

Abdul-raheem Hassan
September 7, 2018

Hukumomi sun tabbatar da samun kwarangwal na mutane da aka binne a rami daya a jihar Veracruz da ke gabashin kasar Mexio mai fama da fataucin miyagun kwayoyi.

https://p.dw.com/p/34SUA
Mexiko Massengrab in Veracruz
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Jami'an tsaro ba su bayyana hakikanin inda aka gano gawawwakin mutanen da aka hako ba saboda dalilai na tsaro, ganin yadda jihar ta shahara da rikicin siyasa da masu tu'ammali da miyagun kwayoyi.

Babban mai gabatar da kara na kasar Mexico Jorge Winckler, ya ce masu bincike na tantance kayyakin mutane 200 tare da katin shaida 144 da aka gano a yankin da aka samu gawawwakin.

A yanzu dai wasu iyalai da suka rasa 'yan uwansu na ci gaba da hako wani kabari da aka gano a shekarar 2016, inda aka samu gawarwaki 280 yayin da wasu 3,600 suka yi batan dabo.