Miliyoyin yara kananan ba sa zuwa makaranta a GTT inji MDD
April 15, 2015Talla
Asusun taimakon yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ya ce talauci da wariyar jinsi da kuma rigingimu da ake fama da su a yankin Gabas ta Tsakiya, sun hana yara fiye da miliyan 12 zuwa makaranta, duk da kokarin da ake na fadada fannin ba da ilimi. A cikin wani sabon rahoto da asusun na UNICEF ya bayar, ya ce akwai karin yara miliyan uku a kasashen Siriya da Iraqi da aka tilasta musu barin makaranta saboda rikicin da ake fama da su a yankin. Ko da yake rahoton na hadin guiwa da UNICEF da sashen kididdiga na hukumar ilimi, kimiyya da al'adu wato UNESCO suka wallafa ya ce yawan yaran da ke barin makaranta a yankin ya ragu, amma ana fuskantar tsaiko a shekarun baya bayan nan.